Boko Haram: Mutane 1500 sun mutu

Shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau da mabiyansa Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kisan mutane 1500 cikin wata uku na nuna tabarbarewar tsaro, a cewar Amnesty

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Amnesty International ta ce akalla mutane 1500 ne suka mutu, a arewa-maso-gabashin Najeriya, a watanni uku na farkon wannan shekarar.

A wani rahoto da ta fitar a ranar Litinin, kungiyar ta ce Boko haram ce ta aikata fiye da rabin kisan, kuma cikin wadanda aka kashen har da 'yan makaranta.

Yayin da martani daga sojojin kasar suka kai kan 'yan kungiyar, ya kara assasa yawan wadanda suka mutu zuwa 1500.

Amnesty ta ba da misalin ranar 14 ga watan Maris, inda ta ce sojoji sun yi amfani da karfin tuwo wajen hallaka mutanen da ake tsare da su 600, wadanda ba sa dauke da makamai.

Kungiyar ta kara da cewa fiye da rabin mutanen fareren hula ne, kuma ta nemi kasashen duniya su yi bincike mai cin gashin kansa cikin gaggawa, kan abin da ta ce ka iya zama laifukan yaki da cin zarafin jama'a.

Amnesty ta yi kira ga hukumar tarayyar Afrika da Majalisar Dinkin Duniya da su yi aiki tare da gwamnatin Najeriya, wajen yin kwakkwaran binciken da ba kumbiya-kumbiya kan laifukan yakin.