An sanya ranakun babban zabe a Masar

Hotunan neman takarar shugaban kasa na Al-Sisi Hakkin mallakar hoto
Image caption Al-Sisi ne ya jagoranci hambarar da shugaba Mohammed Morsi a watan Yulin bara

Za a je zagayen farko na zaben shugaban kasa a Masar a ranakun 26 da 27 ga watan Mayu, a cewar hukumar zaben kasar.

Hakan na zuwa ne kwanaki kadan bayan babban hafsan sojin kasar, Abdul Fattah Al-Sisi ya tube kakinsa, tare da sanar da aniyar tsaya wa takara.

Wakilin BBC ya ce akwai yiwuwar al-Sisi ya samu nasara, saboda farin jininsa da kuma rashin kwakkwaran abokin hamayya.

Idan har bai yi nasara da fiye da kashi 50 cikin dari ba a zagayen farko, za a je zagaye na biyu a ranakun 16 da 17 ga watan Yuni.