An samu Ehud Olmert da laifin cin hanci

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ehud Olmert, tsohon Pirai ministan Isra'ila.

An samu tsohon Pirai ministan Isra'ila Ehud Olmert da laifin cin hanci.

Kotun yankin Tel Aviv ce ta samu Mr Olmert da laifin cin hanci a badakalar wasu filaye lokacin ya na magajin garin birnin Qudus.

Badakalar da aka yayata a shekarar 2008 ce ta tilasta masa sauka daga mukamini Pirai minista.

A shekarar 2012 an same shi da laifin zamba cikin aminci, amma aka wanke shi daga tuhumar almundahana.