Batanci: An yi hatsaniya a Funtuwa

Gwamnan jihar Katsina, Ibrahim Shehu Shema Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption An yi ta kai ruwa rana tsakanin matasa da jami'an tsaron da suka hana kona ainihin makarantar da ta yi jarrabawar

Rahotanni daga garin Funtuwa na jihar Katsina a Nigeria na cewa, an yi wata hatsaniya inda aka kona wata mujami'a da kuma makaranta.

Lamarin ya faru ne bayan wasu matasa sun tunzura, sakamakon wata jarrabawa da suke ganin batanci ne ga sunan Annabi Muhammadu (SAW) da na mahaifiyar sa, da wata makaranta mai zaman kanta ta yi.

Haka kuma rahotanni sun ce wani matashi ya jikkata a lokacin hatsaniyar.

Kawo yanzu dai hankula sun fara kwanciya a garin, inda rahotanni ke cewa an jibge jami'an tsaro musamman a yankin Tudun Wada da lamarin ya faru.