An samu cutar Ebola a Liberia

Hakkin mallakar hoto
Image caption Cutar Ebola na haddasa zazzabi da zubar jini

Hukumar lafiya ta duniya, WHO ta ce mutane biyu sun kamu da cutar Ebola a kasar Liberia da ke Afrika ta Yamma.

Mutanen biyu na zaune ne a gundumar Foya da ke makwabtaka da kasashen Guinea da Saliyo.

A farkon watan nan ne aka tabbatar da bullar cutar ta Ebola mai sanya zazzabi da zubar jini a kudancin Guinea, inda fiye da mutane 70 suka rasu, ciki har da takwas a Conakry, babban birnin kasar.

A zaton cutar ta yadu zuwa Saliyo, abin da ya sa Senegal ta rufe iyakarta da Guinea, wacce 'yan kasuwa ke yawan shige da fice.

Karin bayani