Kotu ta tuhumi Musharraf da cin amanar kasa

Tsohon shugaban mulkin soji a Pakistan, Pervez Musharraf Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption A ranar Litinin kotu za ta duba bukatar Musharraf na zuwa duba mahaifiyarsa a waje

Wata kotu ta musamman a Pakistan ta tuhumi tsohon shugaban mulkin soji na kasar, Pervez Musharraf da laifin cin amanar kasa.

Ana tuhumar Pavez din ne bisa sanya dokar ta baci, tare yin karan tsaye ga kundin tsarin mulkin kasar a shekarar 2007.

Wannan ne karon farko da kotun farar hula, ta taba tuhumar wani tsohon hafsan soji da cin amanar kasa.

Mista Musharraf ya musanta tuhume-tuhume biyar da aka yi masa, in da ya bayyana cewa shi ba maci amana ba ne.