Hukumar lafiya ta duniya ta ce Ebola kalubale ce ga duniya

Ma'aikatan jinyar Ebola Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ma'aikatan jinyar Ebola

Hukumar lafiya ta duniya WHO tace, barkewar cutar Ebola mai saurin kisa a yammacin Afirka shi ne babban kalubale ta fuskar kiwon lafiya da ta taba fuskanta.

Mataimakin shugabar hukumar, Keiji Fakuda yayi kashedin cewa, za a kwashe tsawon watanni hudu nan gaba kafin a ci karfin cutar:

Ya ce, "yana da muhimmancin gaske a dauki matakin wayar da kan jama'ar da wannan cuta ta shafa, domin jama'a su samu cikakkun bayanai a kan cutar.

Ya zuwa yanzu dai cutar ta Ebola ta kashe mutane akalla dari da goma sha daya a kasashen Guinea da kuma Liberia.