Boko Haram: An kama makamai a Kamaru

Hakkin mallakar hoto Nigerian Army
Image caption Wasu daga cikin makaman da jami'an tsaro suka kwace

Hukumomin tsaro a kasar Kamaru sun kwace makamai masu tarin yawa a bata kashi da 'yan bindiga a garin Abugasse dake kan iyaka da kasar Chadi.

Wata sanarwa da rundunar tsaron Nigeria ta fitar, ta ce makaman da aka kwace sun hada da bindigogi 288, makaman roka 35 da kuma wasu abubuwa masu fashewa kusan 35.

Sanarwar da kakakin rundunar tsaron kasar, Manjo Janar Chris Olukolade ya fitar ta ce makaman na kan hanyarsu ta zuwa Nigeria ne don baiwa 'yan Boko Haram damar kaddamar da hare-hare a Nigeria.

A lokacin kamen, an damke mutane biyu a cikin manyan motoci da kuma paspo na kasar Kamaru guda 50.

Sai dai babu wata majiya mai zaman kanta da ta tabbatar da wannan labarin.

Karin bayani