Mata dubu 66 na da kaciya a Birtaniya

Hukumar kiwon lafiya ta Birtaniya Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Za a tura kididdigar farko ma'aikatar lafiya a watan Satumba mai zuwa

An kiyasta cewa akwai mata dubu 66 da ke da kaciya a Birtaniya, kuma mafi yawansu an yi musu ne a wata kasar suna yara.

Kafin yanzu dai, ba a bukatar ma'aikatan lafiya su tara kididdigar wadanda aka yi wa kaciyar, abin da ya sa babu cikkakun bayanai.

An hana yi wa mata kaciya a Birtaniya tun a shekarar 1985, sai dai ba a taba hukunta wani a kai ba.

A makon da ya gabata da ne aka fara shari'ar wani likita a yankin Essex, wanda ake zargi ya yi wa mata kaciya a asibitinsa.

Ana kuma zargin wani mutum a London da karfafa gwuiwar mutane su yi wa mata kaciya.