Binciken BBC game da 'yanci a duniya

Image caption Miliyoyin mutane a duniya na cikin kangin bauta

Wani binciken ra'ayoyin jama'a da sashen BBC mai watsa shirye-shiryensa a kasashen duniya ya sa aka gudanar ya gano cewa kimanin rabin mutanen da aka tuntuba sun gamsu da cewa za su iya bayyana ra'ayoyinsa ba tare da fargaba ba a shafukan intanet.

Binciken ya gano bambance-bambance masu yawa tsakanin kasashe goma sha bakwai din da aka gudanar da shi.

A Nigeria fiye da kashi saba'in cikin dari na iya bayyana ra'ayinsu a intanet ba tare da wani dari-dari ba, yayinda kashi ashirin da biyu cikin dari ne kacal ke da irin wannan ra'ayi a Faransa.

Dangane da batun sa ido daga hukumomi kuwa, mafi yawan wadanda aka nemi ra'ayinsu a Amurka da Jamus na ganin ba su tsira daga sa idon ba, amma fiye da uku cikin hudun wadanda aka tuntuba a China na ganin hukumomi ba sa sa ido kan abubuwan da su ke yi a intanet.

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Karin bayani