Addu'o'in hamdala kan dokar Luwadi a Uganda

Image caption Kasashen Turai dai sun yi barazanar janye tallafin suke ba kasar.

Mabiya addinai daban-daban a kasar Uganda sun gudanar da addu'o'i, domin godiya ga Ubangiji bisa kaddamar da dokar haramta luwadi.

A taron addu'ar da aka yi wa lakabi da godiya ga Allah don kafa dokar hana luwadi, mabiya da shugabannin addinai da kungiyoyin farar hula sun jinjinawa gwamnatin kasar bisa samar da dokar hana luwadi.

Dokar dai ta tanadi cewa duk wanda aka kama yana luwadi da yara kanana da nakasassu a Uganda zai fuskanci daurin rai da rai, kuma duk wani abu mai kama da luwadi shi ma ya zama laifi.

''Mun hadu a nan a zamanmu na 'yan Uganda mabiya addinai daban-daban don nuna goyon bayanmu ga wannan dokar. Wannan wata gwagwarmaya ce ta kubutar da 'yan Uganda don kaucewa fushin Allah Mahalicci'' inji Mufti na kasar Uganda Sheikh Sha'aban Uwaje.

Karin bayani