Za a kwashe musulmi dubu 19 daga Afrika ta Tsakiya

Image caption Musulmi su ne kashi 15% na al'ummar kasar miliyan 4.

Hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce ta na kokarin kwashe Musulmi dubu 19 daga Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya, wadanda ke fuskantar barazanar kisa daga 'yan bindiga masu tsananin kishin addinin Kirista.

Mai magana da yawun hukumar, Fatoumata Lejeune-Kaba ta ce Kiristoci 'yan bindiga na kungiyar Anti-Balaka na barazana ga rayuwar Musulmin kasar.

''Abinda kawai ya hana a kashe baki daya Musulmin da suka rage a kasar shi ne dakarun sojin Tarayyar Afrika da na Faransa. Ga shi kuma ba su da halin tserewa. Su da kansu su ke rokonmu mu kwashe su daga kasar.''

Kungiyar agaji ta Red Cross ta ce kullum lamarin sai tabarbarewa ya ke inda Kirista ke ci gaba da kashe Musulmi, da wawashe dukiyarsu tare da yi wa matansu fyade.

Karin bayani