Mummunar girgizar kasa ta afkawa Chile

Image caption Haka ma ta girgiza wasu dogayen-gine-gine a makwabtan kasashen Bolivia da Peru.

Dubban 'yan kasar Chile ne ke tserewa daga gidajensu a daura da gabar teku, bayan wata girgizar kasar mai nauyin awo 8.2 ta afkawa kasar cikin daren ranar Talata.

Akalla mutane 5 ne jami'ai suka tabbatar da mutuwarsu wasu kuma kamar 7 suka samu raunukka daga bala'in na girgizar kasa da ya afkawa arewacin kasar.

Ko daya ke yankunan da lamarin ya shafa da ba su tagayyara sosai ba, dubbai sun rasa wutar lantarki, yayinda wani filin jirgi ya lalace kuma wasu kasuwanni suka kama da wuta.

''Mun jin kasa na wani motsi mai karfi kamar na tsawon miniti daya ko minti daya da dakika goma sha uku. Hakika girgiza ce mai karfi. A halin yanzu ko'ina ya yi dulum don wutar lantaki ta dauke. Kowa ya fito daga gidansa cikin gari ya koma kango'' inji Kurt Hertramp, wani ganau a garin Arica.

Karin bayani