Ebola ba ta shiga Nigeria ba - Minista

Tutar Nigeria Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption A cewar ministan cutar da ta kashe matar na kama da Ebola, amma ba Ebola ba ce

Mahukunta a Najeriya sun jaddada cewa annobar zazzabin Ebola mai saurin yaduwa, ba ta bulla a kasar ba.

Minista a ma'aikatar lafiya ta kasar Dr. Khaliru Alhasan, ya ce anyi gwajin jinin matar da ake ta yada labarin cewa Ebola ta kashe ta, amma an gano ba cutar ba ce ta kashe ta.

Inda ya kara da cewa suna daukar matakan da suka dace wajen kauce wa bullar annobar a kasar.

Cutar ta kashe akalla mutane 80 a Guinea Conakry, sannan a 'yan kwanakin nan ne aka samu bullar annobar cutar a wasu kasashen yammacin Afrika.

Kamar a kasar Liberia, inda akalla mutane bakwai suka kamu da Ebola mai saurin kisa.

Hukumomin Liberiar sun takaita zirga-zirgar jama'a da ta dabbobi, musamman akan iyakokin kasar da Saliyo da kuma Ivory Coast, domin takaita bazuwar cutar.