An kashe wani Janar a Masar

Image caption An girke jami'an tsaro a habarar inda abubuwan suka fashe

Gidan talabijin na kasar Masar ya ce an kashe wani Birgediya Janar na 'Yan sanda sannan wasu jami'ai 5 sun samu raunuka a sakamakon tashin wasu ababuwa biyu a tsakiyar Alkahira.

Jami'an tsaro sun ce wasu bama-baman da aka dana a gefen titi sun hari 'yan sandan kwantar da tarzomar da aka tura a wajen tsangayar nazarin aikin Injiniya ta jami'ar birnin Alkahira.

Harabar jami'ar ta kasance wani fagen daga tsakanin 'yan sanda da dalibai masu goyon bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi da aka haramta tun bayan da soji suka hambarar da Shugaba Mohammed Mursi a cikin watan Yulin bara, sakamakon wata gagarumar zanga-zanga game da mulkinsa.

Tun daga wannan lokaci 'yan sanda 400 ne aka kashe a fadin cikin kasar ta Masar a wani jerin hare hare, to amma kungiyar 'Yan Uwa Musulmi ta musanta kasancewa da hannu a lamarin.

Karin bayani