Ségolène Royal ta zama minista a Faransa

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Royal da Hollande a wajen kampe

Sabon Firaministan Faransa, Manuel Valls ya kaddamar da sabuwar gwamnati, inda ya kawo Ségolène Royal, tsohuwar abokiyar zaman shugaban kasar Francois Hollande cikin gwamnatin.

Za ta kasance ministar muhalli a wani garan bawul da jam'iyyar 'yan gurguzu ta gudanar bayan shan kaye a zabukan kananan hukumomi.

Fitattu daga cikin ministoci a sabuwar gwamnatin sun hada da Michel Sapin wanda ya zama ministan kudi a yayinda aka nada ministoci mata takwas a cikin gwamnatin.

Laurent Fabius zai ci gaba da rike mukaminsa na ministan harkokin waje a yayinda Jean Yves Drian zai rike mukaminsa na Ministan tsaro.

Karin bayani