'Yan sanda sun kubutar da mutane 42 a Oyo

Jami'an 'yan sandan Najeriya Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Ana cigaba da bincike game da kagon dake dajin da aka yiwa lakabi da mai ban tsoro

Rundunar 'yan sanda a jihar Oyo a Nigeria, tace ta kubutar da mutane 42 daga kangon ginin nan da ake zargi na matsafa ne.

Rundunar tace ta kama wani mutum da ta ce ya yi ikirarin yana amfani da sassan jikin mutane domin sayarwa.

Kangon ginin da ke dajin Soka a Ibadan, ya shafe sama da shekara 10 ana gudanar da harkokin da ake zargi na tsafe-tsafe ne.

A watan Maris ne aka gano kangon ginin dake dauke da rubabbun gawawwaki da kwarangwal da kuma wasu mutane a daure.