An kafa dokar hana fita a Kafanchan

Image caption Gwamnan jihar Kaduna, Mukhtar Ramalan Yero

An kafa dokar hana fita a garin Kafanchan na karamar Jama'a dake Kudancin Jahar Kaduna sanadiyyar wani rikici tsakanin jami'an tsaro da wasu matasa.

Dokar hana fitar ta tsawon sa'o'i ashirin da hudu aka kafa.

Rahotanni na nuna cewa rikicin ya samo asali ne sanadiyyar kama wasu wadanda ake ce Fulani ne dauke da bindigar farauta inda matasan garin kuma a bisa bayanai suka yi kokarin ganin an mika su, don su yanke musu hukunci.

Rahotanni dai na nuna cewa kimanin mutane biyu ne suka rasu,wasu kuma kamar mutane 8 suka sami raunuka a hatsaniyar da ta biyo bayan kama mutanen da bukatar matasan na mika musu su.

Rundunar 'yan sanda ta jahar Kaduna, ta tabbatar da wannan labari to amma kwamishinan 'yan sandan Umar Usman Shehu bai bada tabbacin wadanda suka rasu ba, to amma ya tabbatar da bayanan cewa wasu sun sami raunuka.

Tun bayan harin da aka kaddamar a karamar hukumar Kaura ta kudancin jahar ne dai ake zaman zullumi a wasu sassa na kudancin jahar musamman karamar hukumar ta Jama'a makwabciyar Kaura.

Karin bayani