Sulhu tsakanin Filani da Manoma

Wani bafulani yana kiwo.
Image caption An dai dade ana samun rashin jituwa tsakanin Fulani makiyaya da Manoma, lamarin da kai kai ga asarar rayuka da dukiya.

A Najeriya, kwamitin da babban Sifeto 'yan Sandan Kasar ya kafa domin labubo hanyoyin warware rikicin da ake fama da shi tsakanin fulani makiyaya da kuma manoma a sassa daban-daban na kasar, ya ce ya fara samun nasara wajen sulhunta bangarorin da a baya ba sa ga miciji da juna.

Kwamitin ya ce daga kafa shi a makon da ya gabata har an fara samun fahimtar juna tsakanin Fulani makiyaya da manoma a yankunan da ya ziyarta ya zuwa yanzu.

An dai kafa kwamitin sasantawar ne sakamakon karuwar rikice rikice tsakanin makiyaya da manoma.

Musamman a jihohin Benue da Nasarawa da Katsina da kuma jihar Filato, lamarin da kan haddasa asarar rayuka da dukiyoyi.