'Yan gudun hijirar Syria a Labanon

'Yan gudun hirar Syria a Labanon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Rikicin na Syria dai ya daidata kasar, inda al'umar Syria su ka bar matsugunansu tare da tserewa kasashe makwfta dan neman mafaka.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce a yanzu haka yawan mutanen da suka gujewa rikicin Syria zuwa kasar Labanon sun kai miliyan daya.

Hukumar 'yan gudun hijira ta MDD ta kira adadin da abin da ya zarta misali.

Ta kuma kara da cewa yawan mutanen da ke barin Syria na karuwa a kullum cikin hekaru ukun da aka kwashe ana yaki a kasar.

Babban jami'ain 'yan gudun Hijira na Majalisar Antonio Guterres yace kasar Labanon na fama da yadda za ta yi da mutanen.

Sannan tattalin arzikin kasar ya girgiza, haka nan an samu koma baya ta fuskar kasuwanci da masu yawon bude idanu, ya yin da bukatun al'uma ke karuwa.