Isra'ila ta soke shirin sako fursunonin Falasdinu

Wasu sojojin Isra'ila Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wasu sojojin Isra'ila

Isra'ila ta soke shirin sako wasu fursunoni Falasdinawa domin maida martani kan matakin da Falasdinawa suka dauka na sa hannu kan wasu 'yarjejeniyoyin Majalisar Dinkin Duniya da nufin matsayin yankin mai 'yanci.

Kakakin mai shiga tsakani na Isra'ila, ya shaidawa BBC cewa matsayar da aka cimma akan sabbin fursunonin Falasdinu da za'a sako, an yi ta ne bisa sharadin cewa Falasdinawa ba za su nemi Majalisar Dinkin Duniya ta dauke su a matasyin yankin mai 'yanci ba.

A bara ne aka farfado da tattaunawar zaman lafiya sai dai an samu wasu muhiman batutuwa da bangarorin biyu suka kasa cimma matsaya a kai, wadanda suka hada da batun sakin fursunoni da kuma makomar birnin Kudis.

Karin bayani