Sheik Lemu ya samu lambar yabo a Saudi

Sarkin Saudiyya, Abdallah Hakkin mallakar hoto AFP

Shugaban majalisar amintattu na hukumar taimakon agaji ta musulunci a Najeriya, Sheikh Ahmed Abou Bakr Lemu na Nigeria, ya sami lambar yabo ta kasa da kasa ta sarki Faisal na Saudiyya.

Sheikh Dr. Lemu shahararren masani, mutum ne da ya sadaukar da rayuwarsa ga yiwa musulunci hidima.

Hakazalika mutum ne mai kira ga yin masalaha da sassauci a tsakanin al'umma da kuma bayyana ra'ayinsa akan al'amura ba tare da rufa-rufa ba.

Sheikh Lemu ya bada muhimmiyar gudunmawa wajen kare hakkin mata, haka kuma ya kafa kungiyar Da'awa domin yaki da tsattsauran ra'ayi.