Goodluck da Sanatoci na ta da jijiyar wuya

Senata David Mark Hakkin mallakar hoto davidmark facebook
Image caption Senata David Mark

A Najeriya, wani zaman da majalisar dattawan kasar ke yi na gyara ga kundin tsarin mulkin kasar ya cije sakamakon rashin amincewar da dama daga cikin 'yan majalisar game da wani kauli da ya tanadi cewa duk wani gyaran da za'a yi ga kundin tsarin mulkin sai ya samu amincewar shugaban kasa kafin ya zama doka.

A jiya ne dai 'yan majalisar suka kasa cimma jituwa a kan wannan lamari, inda suka tura batun zuwa ranar Laraba mai zuwa don kada kuri'a a kansa.

Senata Danladi Abdullahi Sankara, dan majalisar dattawan Najeriya ne, ya ce, ba za su amince ba, domin bangaren zartaswa na da tasa rawar, kamar yadda suke da ita.

Sanatan ya bayyana cewa idan suka bari Shugaba Jonathan ya yi musu katsalandan, sun ci amanar wadanda suka zabe su.

Karin bayani