Kotu ta umarci a biya Sanusi N50 miliyan

Sanusi Lamido Sanusi Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption SSS ta kwace fasfon Sanusi a Legas bayan ya dawo daga taron bankunan yammacin Afrika a Nijar

Wata kotu a Nigeria ta umarci gwamnatin kasar, ta biya diyya tare da neman gafara a bainar jama'a, ga shugaban babban bankin kasar da aka dakatar, Sanusi Lamido Sanusi.

Kotun dake zamanta a Lagos ta umarci a biya Sanusi diyyar naira miliyan 50.

Hakan dai ya biyo bayan karya doka da kotun ta ce hukumar tsaro ta farin kaya SSS ta yi, wajen kwace masa fasfo.

A ranar 20 ga watan Fabrairun wannan shekarar ne, gwamnatin kasar ta dakatar da Sanusi daga matsayinsa, bisa zarginsa da almubazzaranci da dukiyar jama'a.

Wasu a kasar na ganin dakatar da shi ba ya rasa nasaba da zargin da Sanusi ya yi, na batan kudaden mai dala miliyan dubu 20, da ba a sanya a lalitar gwamnati ba.