Turkiyya ta dage haramci kan Twitter

Hakkin mallakar hoto afp
Image caption An sanya haramcin kan Twitter ne gabannin zaben da aka yi ranar Lahadi

Gwamnatin Turkiyya ta fara dage haramcin da ta yiwa dandalin sada zumunta na Twitter, bayan kotun tsarin mulki ta ce hakan tauye 'yancin albarkacin baki ne.

Hukumar sadarwa ta kasar ta cire umarnin wata kotu na haramcin da ta sanya a shafinta na intanet.

Ana sa ran nan ba da jimawa ba, masu ziyarar shafin za su iya shiga shafin na Twitter.

Gwamnati ta sanya haramcin ne bayan wasu sun yi tsokaci na zarge-zargen cin hanci da rashawa, da aka danganta da Firai minista Recep Tayyip Erdogan.

Kawo yanzu ba a dage haramcin da aka dora kan shafin You Tube ba, bayan sanya wata murya da aka yi zargin ta ministocin kasar ne, inda su ke tattauna yiwuwar daukar matakin soji a kan Syria.