HIV : Cuwa-cuwa a asibitocin Uganda

Image caption Ma'aikatan asibiti na karbar kudi don bada takardar

Asibitoci masu zaman kansu a Kampala babban birnin Uganda na sayar da takardar shaidar likita dake nuna cewar mutum baya dauke da kwayar cutar HIV, don taimakawa mutane su samu aiki.

Binciken da BBC ta gudanar ya nuna cewar mutane na biyan kudi don a basu takardar shaidar ta bayan fage.

Wakiliyar BBC Catherine Byaruhanga da wasu ma'aikatan BBC sun shafe makwanni suna kokarin gano mutanen da aka baiwa takardun boge dake nuna cewar basa dauke da cutar HIV wacce ke rikidewa ta zama AIDS.

Mutane da dama suna jin tsoron bayyana cewar sun samu takardar ta bayan fage, saboda hakan zai iya shafarsu a wuraren ayyukansu.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana fadakar da jama'a a kan hadarin cutar AIDS

Sarah (ba sunan gaskiya ba) ta ce "Ina da diya amma bani da miji kuma ina bukatar kudi don lura da diyya ta, a don haka shi ne ya sa na samu wannan takardar ta bogi don ci gaba da aiki a wani kamfani".

'Balaguro a Kampala'

BBC ta tattauna da mutane dama wadanda suka sayi takardar shaidar dake nuna cewar basa dauke da kwayar cutar HIV don samun aiki, ko tafiya kasashen waje ko don yi wa abokan zama karya ko kuma don gujewa kyamata daga al'umma.

Mun ziyarci asibitoci 15, kuma daga cikinsu 12 sun amince za su bamu takardun bogi dake nuna cewar bamu da kwayar cutar HIV.

Hakkin mallakar hoto SPL
Image caption Kwayar HIV mai rikidewa ta zama AIDS

Wani ma'aikacin asibiti wanda da farko yace ba zai bamu takardar ba, daga bisani mun sasanta a kan dala 20 don ya bamu takardar shaidar.

Takardun shaidar na dauke da tambarin asibiti, da kuma sa hannu wanda yake nuna tamkar ingantacce ne.

Shekaru ashirin da suka wuce, mutum daya cikin biyar a Uganda na dauke da kwayar cutar HIV, amma lokacin da gwamnati ta soma yekuwar yaki da cutar an samu raguwar mutanen dake dauke da kwayar cutar ta HIV.

Sai dai a yanzu an koma gidan jiya, don kuwa a shekara ta 2005 mutane kashi shida da digo uku ne ke dauke da kwayar cutar, amma a shekara ta 2012 lamarin ya sauya inda mutane kashi bakwai da digo biyu suke fama da cutar a kasar ta Uganda.

Karin bayani