Soja ya harbe takwarorinsa a Amurka

Sansanin Sojin Amurka dake Fort Hood Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sansanin Sojin Amurka dake Fort Hood

Kwamandan Sojin Amurka da ke sansanin Fort Hood a birnin Texas ya tabbatar da mutuwar sojoji uku da kuma wasu goma sha shida da suka ji rauni sanadiyar bude wutar da wani dan bindiga ya yi a sansanin.

Daga baya dan bindigar wanda jami'in Soji ne, ya harbe kansa har lahira.

Janar Mark Milley, kwamandan sansanin yace dan bindigar da ya taba aiki a kasar Iraqi a shekarar dubu biyu da sha daya,na karbar magani saboda yana cikin halin damuwa da bacin rai.

Sai dai ya ce babu wata alama da ke nuna harin na ta'addanci ne, kuma lokaci bai yi ba, da za a tabbatar da dalilansa na kai harin.

Karin bayani