An tsaurara matakan tsaro a Afghanistan

Sojojin Brittaniya a Afghanistan Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Sojojin Brittaniya a Afghanistan

An tsarara matakan tsaro a dukkan fadin kasar Afghanistan kwana guda gabannin zaben shugaban kasa.

Dakarun kasar da na kasashen waje kimanin dubu dari hudu aka girke, a yayinda aka tura jami'an tsaro wuraren da za a kada kuri'ar a tsakiya da kuma wajen kasar.

An datse dukkanin hanyoyin dake isa babban birnin kasar Kabul.

Shugaba Hamid Karzai dai ba shi da damar sake tsayawa takarar shugabancin kasar a karo na ukku don haka za a zabi sabon shugaba.

'Yan kungiyar Taliban dai sun sha barazar kai hari runfunan zabe, Sai dai wasu 'yan kasar ta Afghanistan sun shaidawa BBC cewa duk da wannan barazanar za su kada kuri'a.

Karin bayani