Kotu ta dakatar da bincike kan Sanusi

Image caption Sanusi Lamido Sanusi

Wata babbar kotun tarayya a Lagos ta dakatar da hukumar sa'ido kan kasashe kudade a Nigeria daga bincikar Gwamnan babban bankin Nigeria, Sanusi Lamido Sanusi.

Kotun ta dakatar da yinkurin bincike kan Malam Sanusi wanda aka dakatar daga kujerarsa, har sai an kamalla shari'a kan zarge-zargen da ake masa.

Hukuncin na zuwa kwana guda bayan da a wata shari'ar ta daban, kotu ta umurci gwamnatin Nigeria ta baiwa Sanusi Lamido diyyar naira miliyan 50 tare da neman gafara a bainar jama'a saboda kwaco masa fasfo.

Sai dai hukumar tsaron farin kaya wato SSS ta ce za ta daukaka kara game da hukuncin a kan Sanusi Lamido

A ranar 20 ga watan Fabrairun wannan shekarar ne, gwamnatin kasar ta dakatar da Sanusi daga matsayinsa, bisa zarginsa da almubazzaranci da dukiyar jama'a.

Wasu a kasar na ganin dakatar da shi ba ya rasa nasaba da zargin da Sanusi ya yi, na batan kudaden mai dala miliyan dubu 20, da ba a sanya a lalitar gwamnati ba.

Karin bayani