Tsohon Shugaban Guinea Bissau ya rasu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Margayi Kumba Yala ya rasu yana takarar shugabancin kasarsa

Tsohon Shugaban kasar Guinea Bissau, Kumba Yala ya rasu bayan shafe lokaci mai tsawo yana jinya.

Ya rasu yana da shekaru sittin da daya a duniya sakamakon bugun zuciya.

Kumba Yala ya shafe shekaru uku a kan kujerar mulkin kasar kafin a yi masa cuyin mulkin soji a shekara ta 2003.

Ya kasance malamin Jami'a wanda ya kware wajen magana da harsuna da dama.

Ya rasu kwanaki goma kafin gudanar da zabukan kasar don kawo karshen mulkin soji.