An shiga sabon bincike na jirgin Malaysia

Jiragen ruwa dake binciken Jirgin Saman Malaysia Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Jiragen ruwa dake binciken Jirgin Saman Malaysia

Masu binciken jirgin Malaysian nan da ya bace sun fara wani sabon aiki na bincike a karkashin teku domin gano ko za su jiyo duriyar na'aurar nan da ke adana bayanan jirgi.

Jami'an Astralia da ke jagorantar binciken sun ce wasu jiragen ruwa guda biyu da ke dauke da na'urorin bincike na laturoni su ne za su yi aikin binciken.

Jiragen sama goma sha hudu da jiragen ruwa tara ne za su shiga binciken na yau domin gano jirgin mai lamba MH370 da ya yi batan dabo kusan makwanni hudu.

A yayin wani taron manema labarai gabanin fara sabon binciken Prime Ministan Malaysia Najib Razak ya sake tabbatar ma 'yan uwa da iyalan Pasinjojin dake cikin jirgin saman da ya bace cewar, za a cigaba da bincike har sai an gane jirgin saman

Karin bayani