Microsoft ya fitar da manhajar murya

Cortana Hakkin mallakar hoto Microsoft
Image caption Cortana

Kamfanin manhaja na Microsoft ya kaddamar da wani tsarin da zai dinga taimaka wa masu amfani da wayoyin salula dake da masarrafar Windows.

Manhajar mai amfani da sauti da ake kira Cortana, na amfani da tsarin matambayi na Bing da kuma hanyoyin adana bayanai domin bada damar aiwatar da abubuwa a wayar salula.

Tuni Apple da Google suka fitar da irin wannan tsarin ga masu amfani da iOS da Andriod.

Sai dai wani kwararre a fannin fasaha ya ce, jinkirin da Microsoft ya yi wajen kaddamar da ta shi fasahar, ka iya zama wata hikima.

"Siri da Google na da takaitaccen hanyoyin gane abin da mutum ya fada." A cewar Farfesa Steve Young na jami'ar Cambridge.

"Idan ga misali ka tambayi Siri, abin da ta sani kamar gidan abinci ko wasan kwallon gora, komai zai tafi daidai.

Amma idan ka tambaye ta wani abin da ba a riga an sanya a cikin tsarinta ba, sai kawai ta tura a nemo kalmar a tsarin matambayi."

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Masarrafar Windows 8.1

Ya kara da cewa "Amma na fahimci cewa sai da Microsoft ya yi aiki sosai a kan Cortana, ta yadda da kanta za ta fahimci tsarin jimloli da dama, saboda haka za a iya sa ran cewa za ta aiwatar da abubuwa da yawa."

Shugaban masarrafar Window a wayoyin salula, Phone chif Joe Belfiore ne ya kaddamar da Cortana mai muryar mace a San Francisco.

Za a fara samun Cortana a Amurka, sai Birtaniya da China daga nan kuma sai sauran sassan duniya, inda masu amfani da masarrafar Windows 8.1 a wayoyinsu, za su iya samun Manhajar Cortana idan sun sabunta masarrafar.