Sojoji sun kashe Fulani bisa kuskure

Sojojin Nijeriya Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Sojojin Nijeriya

Rundunar 'yan sandan jihar Nasarawa ta yi karin haske kan kisan wasu Fulani makiyaya a yankin Kiyana na jihar da aka yi da safiyar jiya alhamis.

Kungiyar Miyetti Allah Kautal hore dai ta yi zargin cewa sojoji ne suka kashe mutanen.

Wannan al'ammari dai ya zo ne kwana guda bayan cimma yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin 'yan kabilar Tivi da Fulani makiyaya wadanda ke rikici tsakaninsu a 'yan watannin nan.

Alhaji Ibrahim Idris Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Nasarawa, ya tabbatar wa BBC ta waya cewa lalle sojoji ne suka kashe Fulanin, amma bisa kuskure a lokacin da suke gudanar aikin kakkabe yankin daga 'yan bindiga.

Karin bayani