Nigeria za ta wuce Afrika ta Kudu

Image caption Kamfanin kasashen waje na fitar na mai a Nigeria

Nigeria za ta sauya bayannin kididdigar abinda take samar wa a shekara wato GDP a ranar Lahadi 6 ga watan Afrilu, lamarin da zai sa ta shiga gaban Afrika ta Kudu a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar.

Wakilin BBC Matthew Davies ya yi karin bayani a kan yadda tsarin yake.

Shin menene sauya tsarin?

Majalisar dinkin duniya ta bayyana sauya fasalin tsarin tattalin arziki a matsayin wani "shirin sauya tsarin farashin abubuwa ko kimanta darajarsu ta yadda za a kiddiddige da irin abubuwan da kasar ke samarwa a shekara don sabunta alkaluma". A takaice, za a fitar da sabbin alkaluma a kan abubuwan kididdiga na kasar.

Tattalin arziki abune mai yawan canzawa; yana samun ci gaba, yana durkushewa kuma yana karuwa saboda bayannan wasu sabbin bangarorin tattalin arziki da fasaha da kuma sauyi game da al'umma. Ana amfani da GDP ne wajen gano yadda tattalin arziki kasa ke samun ci gaba a tsawon lokaci.

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kamfanonin sadawar na bunkasa a Nigeria

Alkaluman da ake samu na GDP nada mahimmanci ne kawai idan aka kwatanta da alkaluman da aka samu a shekarar da ta wuce. A takaice, ana sanin GDP na kowacce kasa ne idan aka harhada abubuwan da kasar ke samuwar a jumlace.

Menene mahimmancin sa?

Sauya fasalin kididdiga na da mahimanci saboda tattalin arzikin kasashe na sauyawa bisa shudewar lokaci. Ana samar da karin abubuwa da kuma kirkiro da sabbin fasaha, a don haka sauya fasalin kididdigar zai taimaka wajen fitar da alkaluman da suka yi daidai da lokacin da ake ciki. Yawancin kasashe a duniya na sauya fasalin duk sau daya cikin shekara uku. Amma a Nigeria tsarin kididdigar GDP din ta tun na shekarar 1990.

A can baya, kasar na da kamfanin wayar sadarwa guda daya tal inda akwai layukan waya kusan 300,000. Amma a yanzu masana'antar sadarwa ta bunkasa a kasar, inda akwai miliyoyin layukan sadarwa. A don haka idan ba a sauya fasalin kididdigar ba, to ba za a san ainihin alkaluman da suke daidai ba.

Haka kuma, a shekaru 24 da suka wuce, Nigeria na da kamfani daya tal na sufurin jirgin sama. Amma a yanzu akwai kamfanoni barkatai.

Masu sharhi na ganin cewar, idan aka sauya alkaluman kididdigar aka yi amfani da na shekara ta 2010, GDP na Nigeria zai karu da kashi 65 cikin 100.

Me yasa sai bayan shekaru 24 Nigeria za ta sauya fasalin?

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Danyen mai ne ke samarda da kashi 70 cikin 100 na arzikin Nigeria

A cikin 'yan shekarunan, yawancin kasashen duniya ba sa mayar da hankali wajen gano ainihin alkaluman saboda kashe kudin da za su yi wajen ganowa. Amma a yanzu da aka bude cinikayya tsakanin kasashen duniya, sauya fasalin kididdigar babu wuya musamman ta wajen hukumar kididdiga ta kasa. Kuma a wannan karon shugaban hukumar kididdiga ta Nigeria, Yemi Kale ya ce ba za su yi kasa a gwiwa ba.

Za a ga sauyi na zahiri?

Ga talakawa a kan titi babu sauyi. Don ba za ta canza zani ba. Amma hakan nada mahimmanci ga tattalin arzikin kasa. Don alkaluma za su canza, Nigeria kuma za ta zama kasar da ta fi kowacce a Afrika girman tattalin arziki inda za ta shiga gaban Afrika ta Kudu. Idan aka sauya alkaluman, kididdigar abinda Nigeria ke samarwa a shekara wato GDP zai kasance dala biliyan 432 idan aka kwatanta da na Afrika ta Kudu a wanda yake dala biliyan 370 a shekara ta 2013.

Image caption Dubban yara na talla a kan tituna a Nigeria

Amma kwararru a kan fannin tattalin arziki za su ce Nigeria ba ta taka rawar gani saboda yawan al'ummarta miliyan 170 ne wato ta rubanya Afrika ta Kudu har sau uku. A don haka a yayinda Nigeria za ta bigi kirjin cewar ita ce ta farko amma Afrika ta Kudu tafi ta samarwa da kayayyakin masana'antu.

Shin Nigeria za ta kara jira sai bayan shekaru 24 kafin ta kara sauya fasalin kididdigar?

Ina fata a'a. Ana saran a yanzu za ta dunga yi akai-akai. Ba wai Nigeria kadai ba, Kenya da Zambia suma suna kokarin sake fasalin nasu kididdigar. Sannan kuma kasashen duniya masu bada tallafi na bukatar ganin kasashen Afrika sun gudanar da wannan abu a lokuta da dama don sannin irin taimakon da za su bayar. Amma dai wannan tsarin yana da kyau ga tattalin arzikin kasa.

Alal misali, Amurka na da tsarin sauya fasalin kididdigar tattalin arzikinta a kan lokaci wanda shi ne na daya a duniya. Kamata yayi kowacce kasa ta dunga gudanar na wannan sauyin fasalin akalla sau daya a cikin shekaru hudu.

Karin bayani