An sace 'yan Italiya a Kamaru

Hakkin mallakar hoto AFP

Wasu mutane dauke da makamai a kasar Kamaru sun sace wasu limaman coci 'yan kasar Italiya biyu da kuma wata ma'aikaciyar coci 'yar Canada.

Ma'aikatar kula da harkokin wajen Italiyar ta ce lamarin ya faru ne a arewacin Kamarun -- kimanin kilomita 30 daga iyaka da Najeriya.

Wasu 'yan bindiga biyu ne suka je gidan mutanen da sanyin safiya a cikin wata mota, su ka tafi dasu.

Lamarin ya sa gwamnatin Kamaru da ofishin jakadancin Italiya fara gudanar da aikin hadin gwiwa domin gano su.

Wani kakakin fadar Vatican ya ce Fafaroma Francis ya samu labarin sace mutanen kuma ya na ta yi masu addu'a.

A watan Nuwamban da ya wuce, 'yan Boko Haram sun sace wani fada dan kasar Faransa a kasar ta Kamaru, amma daga basani an sako shi.

Karin bayani