Sojoji sun kona rugagen Fulani a Plateau

Matan Fulani
Image caption Matan Fulani

A jihar Plateau da ke tsakiyar Najeriya Fulani makiyya sun koka kan cewa sojoji sun kona rugage da dama a Dahaye da ke cikin yankin Ganawuri inda a kalla mutun daya ya rasa ransa.

To sai dai kakakin rundunar soji mai kula da tsaro a jahar ta Plateau ya musanta ikirarin da Fulanin su ka yi.

Lamarin ya zo ne a daidai lokacin da Kungiyar Fulani Makiyaya ta kasa Miyatti Allah ke nuna takaicin ta ga harin da sojoji suka kaiwa yankin Kiyana dake jihar Nasarawa a tsakiyar arewacin Najeriya.

Sai dai kuma Alhaji Baba Usman, Sakataren kungiyar Miyetti Allah ta Fulani na kasa ya ce kawo yanzu yarjejeniyar zaman lafiya da suka cimma da mahukunatan kasar na nan duk da cewa an kashe fulani makiyaya da dama a harin da sojoji suka kai ranar alhamis din da ta gabata.

Karin bayani