Ana cigaba da cece-kuce kan taron kasa

Wakilai a taron kasa
Image caption Wakilai a taron kasa

A nijeriya, ana cigaba da taron kasa, inda dukkan wakilan ke ba da shawarwarinsu kan abubuwan da suke ganin yakamata taron ya mayar da hankali a kansa.

Wasu wakilai suna sukar tsare-tsaren da aka yi, musamman rashin ambaton batun tsaro a jawabin da Shugaba Goodluck Jonathan ya yi ga taron.

Manazarta al'amurra a taron sun ce kodayake ba a fara taron gadan-gadan ba, amma suna ganin makudan kudin da aka kashe wajen shirya taron sabanin shawarar da aka baiwa gwamnati cewa taron ba shi da wani amfani, akwai alamun "lauje cikin nadi".

Malam Bashir Baba, daya daga cikin wakilan dake sa ido, sun ce suna zura ido, za su kuma warware nadin, don kowa ya ga laujen.

Karin bayani