An kashe mutane 30 a Zamfara

Hakkin mallakar hoto AP

Jami'an tsaro a Najeriya sun ce an kashe akalla mutane 30 a wani hari da wasu 'yan bindiga su ka kai a wani kauye dake Jihar Zamfara a arewacin kasar.

Lamarin ya faru ne a kauyen 'Yar Galadima sa'adda ake wani taro kan sha'anin tsaro.

Rahotanni sun ce jama'ar yankin ne su ka hadu su na tattaunawa akan yadda za su yi amfani da 'yan banga wajen tabbatar da tsaro a jihar.

Su na cikin taron ne sai 'yan bindigar su ka kai masu hari, su ka kashe akalla mutane 30 daga cikinsu.

Wasu majiyoyi sun ce yawan mutanen da aka kashen sun wuce 30. An kuma jima wasu da dama raunuka.

Rahotanni sun ce an tura sojoji da 'yan sanda zuwa yankin domin kokarin shawo kan lamarin.

Jihar Zamfarar dai ta sha fuskantar hare-hare daga 'yan bindiga.

Karin bayani