Zaben Afghanistan ya yi armashi

Ma su kada kuri'a a zaben Afghanistan Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Su ma mata ba a bar su a baya ba sun fito domin kada ta su kuri'ar.

Al'umar Afghanistan na ta murnar zaben shugaban kasa da aka gudanar cikin zaman lafiya duk da barazar harin da kungiyar Taliban ta ci alwashin kaddamarwa.

Wasu daga ciki sun yi ta taka rawa a kan titunan babban birnin kasar Kabul, ya yin da wasu ke daga yatsan da suka yi dangwalen zaben dan nuna bijirewa barazanar taliban.

Shugaban gidauniyar tabbatar da sahihin Zabe a Afghanistan Nader Nadery ya shaidawa BBC cewa wanna shi ne zabe mafi inganci da aka gudanar a kasar.

Ya kuma ce idan aka duba yadda aka gudanar da zaben ta fuskar yadda mutane suka fito dan kada kuri'a ya fi zabukan da aka gudanar a kasar shekaru goma da suka gabata.

Shugaba Obama ya bayyana zaben da zai maye gurbin Shugaba Hamiz Karzai a matsayin wani babban mataki.

Ya yin da sakataren harkokin wajen Burtaniya William Hague ya bayyana zaben a matsayin babbar nasara.

Jami'an kasar sun yi kiyasin cewa kimanin kashi hamsin da takwas cikin dari na wadanda suka yi rajistar kada kuri'a ne suka fito yin zabe adadin da ya dara zabukan da aka yi a baya.