Nigeria ce mafi karfin arziki a Afrika

Hakkin mallakar hoto BBC World Service

Najeriya ta ayyana kanta a matsayin kasa mafi karfin tattalin arziki a Afrika, inda a karon farko ta ce karfin tattalin arzikinta ya fi na Afrika ta kudu.

Sanarwar ta biyo bayan sauyi ne na yadda ake auna karfin tattalin arzikin kasar.

Ma'aikatar kudin kasar ta ce ba kamar da ba, yanzu ta na la'akari ne da hada-hadar da ake yi a sabbin fannoni, kamar su sadarwa da fasahohin zamani da zirga-zirgar jiragen sama da fina-finai da sauran su.

Sai dai masu aiko da rohotanni sun ce yawancin 'yan Najeriyar na fama da tsananin talauci.

Afrika ta Kudu kuwa, wadda mamba ce a kungiyar G20 ta kasashen dake kan gaba a tattalin arziki a duniya, ta yi wa Najeriyar fintinkau a fannin ababen more rayuwa; kuma talakawanta sun fi na Najeriya samun rayuwa mai inganci.

Karin bayani