Shugaban Ukraine ya kira taron gaggawa

Zanga-zanga a kasar Ukraine Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Zanga-zanga a kasar Ukraine

Shugaban Ukraine Oleksandr Turchynov ya kira taron gaggawa da manyan hafsoshin tsaro, don tattaunawa kan matsalar tsaro a gabashin kasar.

Hakan ya biyo bayan mamayewar da masu zanga-zangar goyon bayan Rasha suka yiwa wasu gine-gine a wasu manyan biranen kasar uku.

A birnin Donetsk, daruruwan masu zanga-zangar sanye da hular kwano da sanduna, sun bangaje shingayen da 'yansandan suka kafa don kaiwa da gine-ginen gwamnatin.

Wasu masu zanga-zangar dauke da tutocin kasar Rasha sun abkawa gine-ginen ofisoshin gwamnati a biranen Kharkiv da Luhansk , kana suka rataya tutocin kasar Rasha a jikin bangon gine-ginen.

Mataimakin Ministan harkokin wajen kasar na gwamnatin wucin gadi Daniylo Lubkivsky ya dora alhakin abkuwar hakan kacokan kan kasar Rasha, yana mai cewa dole sai shugaban kasar ya tsoma baki.