An yi jana'izar mutane 120 a Zamfara

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Su na cikin taron ne 'yan bindiga akan babura su ka auka musu

A Najeriya an yi jana'izar fiye da mutane 120 da aka kashe a harin da 'yan bindiga su ka kai ranar Asabar a Jihar Zamfara.

Hukumomi sun ce kimanin mutane 120 aka kashe a harin da aka kai a kauyen 'Yar-Galadima dake jihar, sai dai mazauna kauyen sun ce adadin ya kai 150.

Hankulan jama'a ya sun tashi sosai a kauyen, inda mata suka gudu, sai maza kalilan suka rage.

Lamarin ya faru ne lokacin da manoma da wakilan kungiyoyin 'yan banga, daga jihohin Katsina da Zamfara da Kebbi da kuma Kaduna ke wani taro kan yadda za su bullo ma hare-haren da a ke kai masu.

Karin bayani