Apo: An bukaci gwamnati ta biya diyya

Image caption Rahoton binciken da aka fitar ya ce an take hakkin rayuwa na wadanda aka kashe

Hukumar kare hakkin bil'adama ta Najeriya, ta ce ta samu rundunar soji da hukumar tsaro ta farin kaya ta SSS da kuma babban lauyan kasar da laifi wajen kisan matasa 8 a unguwar Apo dake Abuja.

Hukumar ta nemi hukumar ta SSS da babban lauyan Najeriya ya biya iyalan mamatan naira miliyan 10 kowannensu, sannan a biya matasa 11 da suka jikkata naira miliyan 5 kowannensu.

Hakan ya biyo bayan binciken da hukumar kare hakkin bil'adaman ta yi game da farwa matasan da sojoji da jam'an SSS suka yi a watan Satumbar shekarar 2013.

Hukumar ta ce babu wata kwakkwarar hujjar dake nuna cewa matasan 'yan Boko Haram ne kamar yadda Hukumar SSS din ta fada.