Assad baida sauran barazana - Hezbullah

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption 'Yan Hezbollah na goyon bayan Assad

Jagoran kungiyar Hezbullah ta Lebanon, Hassan Nasrallah ya ce a ganinsa duk wata barazanar kawar da gwamnatin Bashar Al Assad na Syria ta kau.

Hassan Nasrallah ya fadawa wata jarida a birnin Beirut cewa, barazanar raba kasar ta Syria ma yanzu ta kau, kuma ya ce yana da tabbacin Bashar Al Assad zai sake tsayawa takarar zabe cikin watannin dake tafe.

Wakilin BBC yace "Wadannan kalamai na jagoran Hezbullah na zuwa ne a daidai lokacin da gwamnatin Syria ke kara samun karfin gwiwar cewa, za ta kai labari duk da bore da yakin da ake yi cikin shekaru ukun da suka gabata".

Kusan shekaru uku kenan ana rikici a Syria inda miliyoyin mutane suka rasa matsugunansu sannan dubbai suka rasu.

Karin bayani