'Kira a saki ma'aikatan Al-Jazeera'

Image caption Ma'aikatan uku sun bayyana a Kotu

Kafafen yada labarai sun kara yin kira a saki ma'aikatan Al-Jazeera uku da ake tsare dasu a Masar kwanaki 100 da suka wuce.

Ma'aikatan sun hada da tsohon wakilin BBC Peter Greste wanda aka kama bisa zargin yada labaran karya da kuma taimakawa kungiyar 'yan ta'adda.

Tun a watan Disambar bara aka kama Greste da Muhammed Adel Fahmy da kuma Baher Mohammed.

Dukansu uku sun musanta zargin.

Shari'arsu ta janyo kakkausar suka daga wajen kungiyoyin kare hakkin bil adama da kafafen yada labarai na kasa da kasa.

Akwai kuma wani ma'aikacin sashin Larabci na Al-Jazeera, Abdullah al-Shami wanda aka kama tun a watan Agusta, kuma a halin yanzu yana yajin cin abinci.

Hukumomin Masar na zarginsu da goyon bayan kungiyar 'Yan Uwa Musulmi.

Image caption Ma'aikatan BBC a Moscow na Allawadai
Image caption Masu gabatar da shirin Today na Radio BBC suma sun nuna damuwa

Karin bayani