An kashe limamin coci a Homs

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fadar Vatican ta nuna damuwa game da kisan

A birnin Homs dake cikin tsaka mai wuya, an kashe wani dattijo dan kasar Holland wanda ya sadaukar da rayuwarsa ga aiki a Syria.

Kungiyar da yake yi wa aiki mai suna Dutch Jesuit ta ce, wasu 'yan bindiga ne suka aukawa gidan da dattijon yake suka fito da shi bakin titi da karfin tsiya kana suka harbe shi.

Shi dai limamin cocin Roman Katolikan mai sun Frans Van Der Lugt, ya zabi ci gaba da kasancewa a garin Homs da aka yi wa kofar rago ne, yana cewa, zai ci gaba da kasancewa da mabiyansa, har sai dukkansu sun samu damar ficewa daga birnin.

Tuni dai fadar Vatican ta ce, marigayin ya mutu a matsayin mai son zaman lafiya.