An fara zaben majalisar dokoki a India

Dogon layin masu kada kuri'a Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Batun cin hanci da rashawa da hauhawar farashin kayayyaki ne ya kankane yakin neman zaben kasar

An fara zaben majalisar dokoki wanda za a dauki tsawon wata guda ana yi a kasar Indiya.

A ranar Litinin wato ranar farko ta kada kuri'ar, an samu dogayen layuka tun kafin bude rumfunan zabe.

Fiye da mutane miliyan 800 ne suka cancanci jefa kuri'a, a tsawon makonni biyar din da za a yi ana zaben.

Jam'iyyar Congress mai mulki na fuskantar babban kalubale daga jam'iyyar Hindu BJP, ta masu ra'ayin 'yan mazan jiya.