NEMA ta fara rabon kayan agaji a Borno

Wadanda rikicin boko haram ya shafa na kabar agaji Hakkin mallakar hoto NEMA
Image caption Mutanen da rikin ya shafa na cikin mawuyacin hali

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Najeriya, NEMA ta ce ta fara raba kayan agaji ga mutanen da rikicin Boko Haram ya shafa, a wasu sassan jihar Borno.

Yankunan da aka fara rabon kayayyakin agajin sun hada da Mainok da Jakana, wadanda suka yi fama da hare-haren da ake zargin kungiyar Boko Haram da kai wa a kwanakin baya.

Al'ummomi da dama da rikicin Boko Haram din ya shafa na korafin cewa, ba sa samun wani taimakon a zo a gani, daga gwamnati ko daidaikun jama'a.

Mutane miliyan uku ne aka yi kiyasin na bukatar agajin gaggawa, akasarinsu mata da kananan yara a jihar ta Borno.