Rwanda na makokin tunawa da kisan al'umma

Hakkin mallakar hoto
Image caption Faransa ta janye daga makokin bayan shugaba Kagame ya zarge ta da hannu a kisan kiyashin

Al'ummar Rwanda sun fara makokin mako guda, domin nuna alhini game da kisan al'umma da aka yi a kasar, shekaru 20 da suka wuce.

Shugaban kasar Paul Kagame ya kunna wata wuta da za ta kai kwanaki 100 tana ci, daidai tsawon kwanakin da aka dauka ana kisan mutane a wancan lokaci.

Akalla mutane 800,000 aka kashe a lokacin tashin hankalin, kuma mafi yawa daga cikinsu 'yan kabilar Tutsi ne, sai 'yan kabilar Hutu masu matsakaicin hali.

Kisan da 'yan Kabilar Hutu masu tsattsauran ra'ayi suka aikata a shekarar 1994.