Zamfara: Za a yi shawagi da jirage

Hakkin mallakar hoto Aliyu
Image caption Ba wannan ne karon farko da jami'an tsaro suka ce za su yi amfani da jirage wajen tabbatar da tsaro a yankin ba

Babban sifeton 'yan sandan Nigeria, Muhammad Dahiru Abubakar ya umarci jami'an rundunar su fara shawagi da jiragen sama a jihar Zamfara, domin tabbatar da tsaro.

Sanarwar da kakakin rundunar, Frank Mba ya fitar ta ce an tura wata rundunar 'yan sandan kwantar da tarzoma da masu yaki da ta'addanci, zuwa jihar Zamfara domin fafatawa da maharan da ke addabar al'ummar yankin.

A karshen makon jiya ne dai wasu mahara suka kashe akalla mutane 120 a jihar ta Zamfara, baya ga hare-haren da aka jima ana kai wa kauyukan jihar da makwabtanta.

Sanarwar, ta kuma bukaci al'ummar yankin su hada kai da jami'an tsaron domin tabbatar da zaman lafiya.

Karin bayani